GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA SHA RUWAN DUWATSU




Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya sha ruwan duwatsu  ga wasu gungun matasa masu goyon bayan Jam'iyyar APC a garin Gusau hedikwatar Jihar.

Wannan ya biyo bayan shigowa  da yayi da tawagar sa a lokacin da Magoya bayan "yan takarar gwamna a karkashin Jam'iyyar APC a jihar har su bakwai suka tarbo su daga garin 'Yankara dake iyaka tsakanin Jihar Katsina da ta Zamfara.

Da muke zantawa da wani da abun ya faru a gaban sa yace gwamnan yana zuwa sai matasan suka fara ihu suna kiran shi da 'barawo....barawo bamuso ....bamu so! Abun yayi kamari har sai da jami'an tsaron sa suka yi ta harba bindiga a sama domin korar wadannan matasa.

Idan baku manta ba, siyasa a jihar Zamfara tayi zafi inda shi gwamnan ya ayyana cewa kwamishinan kudin Jihar zai gaje shi wanda wannan hukuncin bai yi wa sauran yan takarar dadi ba wanda shine dalilin da ya sa suka hadu wuri daya domin tunkarar wanda gwamnati ta tsayar.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA