GASKIYAR ABINDA KE FARUWA A DAJIN ZAMFARA.
Daga Mustapha Sarkin Kaya
A safiyar Assabar Hadakar Kungiyoyin Sakai da suka hada da Yan Farauta da Maharba, Daga Arewacin Zamfara da gabashin Sakkwato Suka Shiga Dajin da ya hada Zamfara da Sakkwato wato Dajin Gundumi Inda aka kwashe yinin Jiya Assabar Ana fafatawa.
Duk dayake Wannan Aiki yasamu matsala ta hanyar Rashin Shigar Sirri, domin Mahara Sun samu labarin zuwan Yan sakai tun a lokacin da suke kan hanyar Shiga Dajin, wannan lallai ya sababba kwantan 6auna da 6arayin sukayi, a karon farko lallai sunyi barna ga Gungun yan sakai Musamman ga Wadanda sukayi kokarin Dawowa baya.
Amma yazuwa Yau lahadi Akwai labari Mai kyau akan wannan fafatawa Ansamu galaba sosae, yazuwa Yanzu Mun samu labarin Mashuna fiye da Dari biyu da aka kona tare da kashe 6arayi da ba'asan adadi ba. An karbo bindigogi Ak47, fiye da Saba'in, an karbo Manyan bindigogi Masu Jigida, kuma har Yanzu Suna bakin fama.
Ansamu Gungun wasu Yan sakai da suka Hadu da Safiyar Yau Lahadi a Garin Teke da ke Cikin Sabon birni, Sun Sake Shiga Daji domin karawa Wadanda suka Shiga Jiya karfi.
Sudae Wadanda suka Shiga Jiya Suna kirarin akaro Masu karfi ne domin Sunajin kamshin galaba kan 6arayi.
Abinda yake Daukar Hankalin Al'ummar wannan yanki Shine. Akwai Daruwan sojaji Da aka turo domin bada tsaro Amma lallae basu goyi bayan wannan tafiya ba.
Suna gari kwance Wanda Al'umma suke ganin Zaiyi kyau a Shiga Daji dasu Domin kara Inganta wannan aiki ko bakomai Sune suka kware kuma sukasan makamar aiki.
Comments
Post a Comment