NAIRA DUBU BIYAR (N5,000) AKE BIYANA A DUK LOKACIN DA NA SHIRYA AKA KAI ƘUNAR BAKIN WAKE, INJI WANI WADA...
Daga Shafin Datti Assalafiy
Wani wada ɗan kungiyar boko-haram da aka kama mai suna Abubakar Kori, wanda yake shirya yadda ake kai harin ƙunar bakin wake yace Bai taɓa karɓan kasa da naira dubu biyar ba akan kowace harin ƙunar bakin wake da yake shiryawa yan ta'addan kungiyar boko-haram a birnin Maiduguri.
Abubakar Kori, ɗan shekara 25 yana ɗaya daga cikin mutane 22 da jami'an ƴan sanda suka kama a jihohin Borno da Yobe, sakamakon samun su da hannu da akayi wurin kai hare-haren ƙunar bakin wake da ƴan ta'addan boko-haram keyi.
Ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa naira 5000 ake biyan shi a duk lokacin da ya shiryawa ƴan ta'addan yadda zasu kai hari tare da samun nasara, a birnin Maiduguri da kewaye.
Abubakar Kori, Wanda shi mai gadi ne a wani gidan mai a yankin unguwar Dalori dake birnin Maiduguri, Yace yana da hannu a wasu hare-haren ƙunar bakin wake da aka gudanar a ƴan kwanakin nan a birnin na Maiduguri. ~Isa Ade
Allah Sarki, wato jama'a ina yawan tuna rubutun da nayi na karshe a rayutawa ana gobe za'aci amanata aje a boyeni a karkashin Kasa, rubutun da nayi a wancan lokacin shine mai taken SUN MAYAR DA TA'ADDANCIN HANYAR NEMAN KUDI rubutun da ya tayar da hankalin maciya amana.., shi wannan wadan ma da ake bashi dubu biyar kacal a matsayin kasonsa ai bai samu komai ba a abinda yake fita na makudan kudade karkashin wannan ta'addancin da maciya amana basa kaunar ya kare
Hakika dole na sake yin jinjina ga DCP Abba Kyari da rundinarshi bisa namijin kokarin da sukayi wajen cafke wadannan muggan 'yan ta'adda masu hatsari da suka buya a cikin al'umma.
Don Allah 'yan uwana musulmi mu dinga saka DCP Abba Kyari cikin addu'ah Allah Ya tsareshi daga dukkan sharrin maciya amana kamar yadda akaci amanar Sarkin Yaki Abu Ali Allah Ya jikansa da rahama Ya karbi shahadarsa Amin.

Comments
Post a Comment