MATSALOLIN TSARO: Majalisar Dokokin Jahar Zamfara ta umurci Sakatariyar ta da ta rubuta wasika zuwa ga ministan Tsaro


-------------------------------------------------------------------

Majalisar dokokin Jahar Zamfara ta umurci Sakatariyar ta da ta rubuta wasika zuwa ga ofishin Ministan Tsaro domin kara sanar dashi halin  rashin tsaro da ya addabi mutanen wannan Jiha.

Dan Majalisa mai wakiltar Maru ta Kudu wato Hon Abdullahi Mohammed Dansadau ne yayi wannan kira a lokacin wani zama da Majalisar tayi na gaggawa a ranarAlhamis.

Hon Dansadau ya roki gwamnati tarayya da ta juyo da hankalinta a Jihar Zamfara ta hanyar turo karin Jami'an tsaro da yawa domin ganin an samu kai karshen matsalar tsaro da ta addabi jama'ar wannan jihar musamman yankin da yake wakilta.

Hon Aliyu Ango Kagara shi ya goyi bayan wannan kuduri wanda daga baya Hon Malam Mani Mummuni ya kara goya  mashi baya.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA