Posts

LARURAR DANNAU WATO SLEEP PARALYSIS

Image
  Daga Ibrahim Y. Yusuf Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu ahalin bacci, yakan iya faruwa sau daya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan rika fuskantar yanayin akai-akai. Yanayi ne me kama.da mutuwa duk da yakan kasance mutum na acikin hayyacinsa farke saide sam yakan rasa ikon motsawa ko magana.  Wani lokacin ma yakan zamo idon mutum abude zahiri duk da cikin bacci yake; abunda wasu kan kira da bacin zomo... toh saide hakan duk baisa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa yana cikin mawuyacin hali ko yana bukatar dauki an maquresa. Shiyasa ga duk meson fahimtar me ake nufi da FIRGICI toh dannau shine cikakken misalin firgici ko ince ihunka banza domin ko ihun kayi ba'a ji, ba'a san ma kanayi ba  ALAMOMIN DANNAU Mutane kan fuskanci ma bambantan alamu; Saide duk yana daga alamun dannau ya zamto: ■- Mutum yaji kamar annan-naɗesa cikin wani bargo me nauyi, ko kamar anɗaure hannuwa da kafafunsa a mike kamar gawa, wasu kuma suji kamar anshakesu sun...

YADDA TURAWA SUKE KOKARIN KAFA KASAR ISRA'ILA HAKA NE SUKA KAFA AMERIKA DA SAURAN WASU KASASHE

Image
Malam Aminu Aliyu Gusau Tun daga shekarar 1887 lokacin da turawa, musamman turawan Biritaniya, suka fara kawance da yahudawa a kan manufar kwace kasar Falasdinu, har zuwa yau , zamu ga cewa babbar manufarsu itace kwace kasar ta Falasdin baki daya da kore dukkan Falasdinawa daga cikinta. Ma'ana dai itace dukkan tattaunawa da ake yi a Majalisar dinkin duniya da wadda kasashen turawa suke yi game da samar da wata kasar Falasdinawa gefen kasar yahudawa munafunci ne ba gaskiya bane. Dama kawai suke son samu domin su idar da aikin da suka fara na kawar da dukkan Falasdinawa daga dukkan kasar ta Falasdin. Wannan hanya da turawa da yahudawa suke bi a Falasdin ba nan ne suka fara haka ba. Sun yi haka a wasu kasashe, suka kwace su daga mazaunansu na asali, ta hanyar kashesu da dannesu da korarsu. Daga cikin irin wadannan kasashe da turawa suka shiga suka kashe mafi yawan mazaunansu, suka danne sauran, suka mayar da kasar tasu, akwai Amerika da Australiya da Greenland. A Afrika ma sun yi koka...

Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Koda

Image
  ✅Kauce wa shan magani barkatai ✅Daina amfani da magani ba tare da umarnin likita ko masanin kiwon lafiya ba ✅Ziyartar asibiti duk lokacin da ake fama da wani rashin lafiya ✅A rungumi dabi’ar shan ruwa da yawa, saboda hakan na taimaka wa aikin koda ✅Takaita cin gishiri a abinci ✅Yawaita ta’ammali da ’ya’yan itatuwa ✅Guje wa yawan cin abincin gwangwani, da danginsa. Allah Ya bamu lafiya.

Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ahmad Gulak A Imo

Image
  Dubun gudajjen sojan da ke jagorantar hare-haren sari-ka-noken IPOB ya siffanta yadda ya kashe Ahmed Hula, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa. Yan sanda sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaban kasa a bangaren siyasa na zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Michael Abattam, ya ce Las Kofur Nwangwu Chiwendu, wanda dubun tasa ta cika ya gudu ne daga aikin soja ya shiga kungiyar ’yan ta’addan. A lokacin da aka yi holen sa a hedikwatar ’yan da ke Owerri a ranar Laraba, ya shaida wa ’yan jarida cewa ya shiga aikin soja a 2013, amma bayan ya samu kwarewa a fannin sarrafawa da gyaran manyan makamai, sai ya tsere a 2021 ya shiga kungiyar IPOB. “Ya zama Kwamanda a reshen soji na IPOB (ESN) inda ya horas da ’yan kungiyar sama 1,000 kan sarrafa makamai da kai hare-haren ta’addanci. “Ya amsa laifin kai hare-hare kan ofishoshin ’yan sanda da gine-ginen gwamnati a jihar nan,” in ji kakakin ’yan sa...

SOJOJIN NAJERIYA SUN FATATTAKI YAN TA'ADDA A JIHAR ZAMFARA

Image
 Dakarun sojin Najeria sun samu nasarar fatattakar "Yan ta'adda a kauyen Malele dake Masarautar Dansadau a Karamar hukumar mulkin Maru dake Jihar Zamfara. Rahotannin da muke samu daga kauyen sun nuna cewa a jiya Lahadi daruruwan maharan saman babura fiye da 400 sun dauki aniyar kai hare-hare a kauyen Malele da sauran kauyuka da ke zagaye amma hakan bai samu ba saboda dauki da Sojojin sama tare da taimakon na kasa da suka kai. Mutanen kauyukan dake kusa da wurin da abun ya faru sun tabbatar da ganin gomman gawarwakin wadannan "Yan ta'addan tare da baburan da suka hau zuwa wajen kai wannan farmakin da bai samu nasara ba, haka kuma sun shedi ganin wadanda suka ji rauni a kan babura suna gudu. Allah Ya cigaba da ba Sojojin Najeriya nasara.

Boka Ya Harbe Mai Neman Maganin Bindiga Har Lahira

Image
  ’Yan sanda a Jihar Enugu sun damke wani boka da ake zargi ya harbe wani da ya nemi maganin bindiga a wurinsa a yankin Karamar Hukumar Isi-Uzo. Aminiya  ta samu rahoton cewa, bokan ya harbe mutumin har lahira a lokacin da yake kokarin jarraba ingancin maganin bindigar da ya hada masa. Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Talata cewa, bokan ne ya kera bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe mutumin. Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna bokan ya amsa cewa lallai ya yi amfani da bindiga kirar gida wajen harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutumin a inda yake sana’arsa ta tsubbace-tsubbace. Bokan ya ce hakan ya faru ne lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada wa marigayin. Ndukwe ya ce batun na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar inda ake ci gaba da bincike.

MATSALAR TSARO A JIHAR ZAMFARA: IDAN BERA DA SATA.............

Image
Daga Sanusi Bello Dansadau Lalacewa takai matuka akama basarake wanda shine uban al'umma da hannu a cikin  lamarin kashe-kashen mutane da garkuwa dasu don kudin fansa to me ya rage Gwabnati tayi ko me mu keso ta yi?  A halin yanzu babu gari guda dake da yawan al'umma da ya kai 5000 face sai an samu masu hannu a cikin lamarin 'yan ta'addar nan wasu ma an sansu. Yakamata muyi wa kanmu fada ba Gwabnati kadai keda alhakin kawo tsaro ba muma amataki na daidaiku da al'umma munada rawar da zamu taka. Ya Allah ka tona asirin duk mai alaka da barayin nan ya Ubangiji allah ka sako mashi/su babban bala'i daga gareka Allah kayima talakka gata ka yaye muna wannan musifa amin.