Posts

Showing posts from February, 2022

ZAMAN GWANNONIN APC DA SHUGA BUHARI

Image
  Shugaban kasa Buhari ya shawarci a yi sasanci wajen zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa Gwamnoni kuma sun aminta da tsarin karba-karba na shugabancin jam'iyyar da ya dawo Arewa A taron shugaban kasa Buhari da gwamnonin jam'iyyar APC, da ya gudana yau Talata, kan yadda za a gudanar da zaben sabbin shuwagabannin jam'iyyar a matakin kasa, shugaban kasa Buhari wanda shi ne jagoran taron, ya bayar da shawarar cewa, ba zabe yakamata a gudanar ba, game da shugaban jam'iyyar, kamata ya yi masu neman kujerar su zauna su sasanta kansu su bar wa mutum daya, saboda tabbatar da hadin kan junansu. A taron kamar yadda Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana wa manema labarai bayan kammala taron ya ce, shugaban kasa Buhari ya buga misali da cewa tun da aka kafa jam'iyyar APC ba a taba zaben shugaban jam'iyyar ba, sai dai a yi sasanci a bar wa mutum daya "Bisi Akande shi ne shugaban jam'iyyar APC na farko, kuma an zabe shi ne ta hanyar sasanci, haka shima  John Oyegun a z...

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA KAI GAISUWAR TA'AZIYA A KARAMAR HUKUMAR ZURMI

Image
  Daga Muawiya Zurmi Yau ne Midaraja Gwamnan Jihar Zamfara Hon (Dr) Bello Matawallen Maradun yayi ta'aziyar mutane 8 da ƴan bindiga sukayi garkuwa dasu a tsakiyar daminar da ta gaba ta kuma daga baya suka kashe su bayan kwashe tsawon wata takwas a hannun su Gwamna yayi ta'aziyar ne ta hannun kwamiti mai karfi daya kafa domin suje suyi ta'aziya ga yan uwa da abokan arzikin wadanda suka rasa rayukan su kwamitin dai yana karkashin jagorancin Hon Abdullahi Muhammad Gurbin Bore Talban Zurmi da memmobinsa da suka hada da Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Zurmi Hon Dr Auwal Bawa Moriki, Mai ba Gwamna Shawara Hon Abubakar Justice Dauran da sauran muhimman mutane.

INA MAKOMAR SIYASAR ABDULAZIZ YARI, MARAFA DA MABIYAN SU?

Image
A satin da ya gabata ne daya daga cikin shugabanin "yan awaren APC reshen Jihar Zamfara wato tsohon Sanata Kabiru Garba Marafa ya kai ziyara a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa dake Abuja domin tantance katin shi na zama cikakken dan Jam'iyyar APC. Isar sa ke da wuya ya tafi kai tsaye zuwa wurin rumbun adana bayanai na daukacin wadanda suka yi rejistar wannan jam'iyyar wato APC inda ya umurci mai bincike da ya bincika masa sunan shi ta hanyar lambobin katin rejistar shi. Bayan kammala bincike kwakwaf da aka yi daga rumbun ajiyar, babu alamar suna ko lambar wannan rejistar shi ba a rumbun adana bayanai na wannan jam'iyyar. Rahotanni sun suna tsohon Sanatan ya fusata ya fita yana zage-zage. Idan baku manta ba bayan sauya shekar da Gwaman Bello Matawalle yayi daga Jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyyar APC hedikwatar Jam'iyyar ta bukaci kowa ya sabunta rijistar shi ta zama cikakken dan Jam'iyyar yayin da bangaren 'Yan awaren suka yi kememe suka ce ba zasu can...