SHUGABA BUHARI DA HAUSAWA
Daga Muhammad Bin Ibrahim Zuwa yanzu, abin da ke bayyana a tsakanin Hausawa, al'ummar da ta nuna qulafucin so ga Shugaba Muhammadu Buhari fiye da yadda ta nuna wa kowane mahaluki a duniya, shi ne nadama. Nadama a kan zaben tumun daren da suka yi. Saboda sun farga cewa abin da suka tsammana a tattare da shi ba haka ba ne. Yanayin nadama mummuna ne, don haka wanda ya samu kansa a ciki abin tausayi ne koda kuwa da gangan ya sa kansa tun a tashin fari. Sai dai kuma, kamar yadda kowane yanayi mai kyau yake da bangarensa mara kyau, haka ma kowane yanayi mara kyau yake da bangare mai kyau. Halin da mu Hausawa muke ciki a yau game da batun shugabanci, hali ne mara kyau da dadi, don mun fi sauran al'ummomin qasar fuskantar uquba, amma kuma halin yana tattare da guzirin busharar farin ciki a gare mu in har muka yarda muka amfana da yanayin ta hanyar tsara lamurranmu da kyau. Yanzu mun gane cewa, gaskiyar mutum ko da'awar gaskiyarsa, ba su ne kadai ababen buqata ga shugaba mai kaman...