INA MAKOMAR TSARON NAJERIYA?
Daga Datti Assalafiy Majalisar Dattawa da sauran al'ummar Kasa suna cigaba da yin kira ga Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya akan ya tsige manyan hafsoshin tsaron Nigeria, tare da maye gurbinsu da sabbi A nazari da tunanin masu wannan kiran ga shugaba Buhari shine cews idan ya aiwatar da bukatarsu hakan zai zama sanadin magance matsalar tsaron Nigeria a halin da ake ciki To amma ga mutanen da suka san sirrin tsaron Nigeria zasu tabbatar muku da cewa tsige shugabannin tsaro da maye gurbinsu da wasu sabbi ba zai canza komai ba, ko da za' samu canji na lokaci ne kankani lamarin tsaron Kasar zai cigaba da tafiya a yadda yake Amma ina ne matsalar tsaron Nigeria yake? kuma ta ina za'a magance matsalolin tsaron? Ku daure ku karanta wadannan mas'alolin tsaron Nigeria guda sha-shida (16) wanda ni Datti Assalafiy dalibin jami'ah dake karatu a fannin kimiyyar Laifuka da Tsaro na wallafa kamar haka: ! (1) Duk wanda ke son fahimtar wannan sai yayi ...