Posts

Showing posts from November, 2018

HUKUMAR YAKI DA SHAN MIYAGUN KWAYOYI SUN KAMA YAN SANDA BIYU SUN RAKA ALBURUSAI ZUWA JOS

Image
Hukumar hana sha da yaki da miyagun kwayoyi ta bada sanarwar jami'an ta sun kama wasu jami'an 'Yan Sanda su biyu akan hannu da suke da shi wajen shigo da alburusai guda Dubu Daya da Dari biyu da Hamsin (1250). Da yake bada bayani ga taron 'Yan Jaridu a ranar Talata 27/11/2018, Mai magana da yawun hukumar Jonah Achema yace sun kama wadannan alburusai ne lokacin da suke gudanar da zirga-zirga akan karshen hanyar Gwgwalada-Abaji zuwa Lokoja. Kamar yadda yayi bayani, alburusan an aiko su ne daga Lagos ta hannun wani kamfanin zirga-zirga wanda ya nuna wadannan "Yan sanda guda biyu zasu karbi kayan. An kama " Yan sandan biyu wato Mataimakin Sufitandan 'Yansanda (ASP) Jacob Jalwap wanda yake aiki a Helkwatar "Yansanda a garin Jos da kuma Kofur (Cprl) Nadul Seizing da yake aiki a Unguwan Rogo dake garin Jos a kan bincike da ake na shigo da wadannan alburusai wanda takardar dake nuni da wanda zai amshi kayan ta nuna sunan Kofur Nadul Seizing da ku...

MATSALAR TSARO A JIHAR ZAMFARA: IDAN BERA DA SATA.............

Image
Daga Sanusi Bello Dansadau Lalacewa takai matuka akama basarake wanda shine uban al'umma da hannu a cikin  lamarin kashe-kashen mutane da garkuwa dasu don kudin fansa to me ya rage Gwabnati tayi ko me mu keso ta yi? A halin yanzu babu gari guda dake da yawan al'umma da ya kai 5000 face sai an samu masu hannu a cikin lamarin 'yan ta'addar nan wasu ma an sansu. Yakamata muyi wa kanmu fada ba Gwabnati kadai keda alhakin kawo tsaro ba muma amataki na daidaiku da al'umma munada rawar da zamu taka. Ya Allah ka tona asirin duk mai alaka da barayin nan ya Ubangiji allah ka sako mashi/su babban bala'i daga gareka Allah kayima talakka gata ka yaye muna wagga musifa amin.

ZAMU KORI MA'AIKATA IDAN SAI MUN BIYA DUBU TALATIN (N30'000)

Image
Ba zamu iya biyan karancin albashin ma'aikata har Dubu Talatin (N30,000)ba, idan akace sai mun biya to lallai zamu kori ma'aikata. .........inji Abdulaziz Yari Abubakar Gwamna Jihar Zamfara.

HIRAR HASANA DA HUSAINA DA SUKE HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE

Ku saurari hirar da akayi tsakanin daya daga cikin yan Matan nan  Hasana da Husaina da aka sace a Jihar Zamfara. Ya Allah Ka kubutar dasu da duk sauran Musulmi amin.

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA MALAM ABDUL'AZIZ YARI

Image
Daga Datti Assalafiy Assalamu Alaikum. Da farko ina yiwa Maigirma Gwamna jaje bisa abinda yake faruwa a jihar Zamfara kuma a matsayinka na babban jami'in tsaro na jihar Zamfara, wannan itace hanyar da Datti Assalafiy zai iya baka wasu shawarwari na tsaro wanda za'abi a magance matsalar da yake faruwa da taimakon Allah Abin tsoro ne duk ranar da na ziyarci wannan dandali na facebook sai na ga sanarwa anyi garkuwa da mutane a Zamfara, yanzu matsalar ta fara shigowa har Katsina Maigirma Gwamna ina son ka san da cewa manyan kungiyoyin 'yan bindigar da suka addabi Jihar Zamfara sun samu nasara kulla alaka na kasuwanci tsakaninsu da 'yan ta'addan jejin Sambisa, dama tun shekaraun baya jagoran 'yan ta'addan ya taba neman hanyar da zai kulla alaka dasu bai samu ba sai a yanzu Kafin wannan alaka na kasuwanci ta kullu 'yan bindigar da suka mamaye Jihar Zamfara sai sun tafi har kasar Libya kafin su sayo bindiga da hardashin bindiga, kuma da tsada s...

ARANGAMAR 'YAN SHI'AH ZAKZAKIYYAH DA JAMI'AN TSARO: ZUWA GA MALAM YAKUBU YAHAYA KATSINA

Image
Daga Malam Aminu Aliyu Gusau. Da yake na fi shekara 20 rabona da saduwa da kai , ina fatar kana cikin koshin lafiya . Ina kyautata zaton kai ne wakilin Mal. Alzakzaki na kasa duk da ban iya tantancewa . Amma dai ko da ba kai bane to kana da matsayin da zan iya rubuta wannan makala zuwa gareka a cikin kungiyarku ta IMN . Ina fatar zaku duba wannan makala da idon basira , ki kuma yi tunani a kai. A halin gaskiya a matsayinku na shugabanni ya kamata ku daina ci gaba da tura matasa bisa tituna ana salwantar da rayuwarsu, Musamman ganin cewa tun daga 2015 bayan waki'ar Zariya duk wadanda ake kashewa a cikin muzaharorinku ba a taba kashe wani shugaba ko jigo ba , banda Mal. Kasimu Umar Sokoto, matasa ne maza da mata kawai kuke turawa ana hallakasu .  Malam so da yawa mu kan so mu zargi sojoji da jami'an tsaro akan yadda suke budewa mabiyanku wuta akan tituna , ko mu zargi gwamnatin da sukewa aiki , amma alal hakika idan muka yi la'akari da irin yanayin tsokana da ...