Posts

Showing posts from May, 2018

SARKIN MALAMAN GUSAU MALAM IBRAHIM WAKKALA YA RABA KAYAN AZUMI GA AL'UMMAR JAHAR ZAMFARA

Image
Ranar Litinin 28/05/2018 wanda yayi daidai da 12 ga watan Ramadan Mataimakin Gwamnan Zamfara Sarkin Malaman Gusau Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman ya raba kayan azumi tare da kayan sallah ga mutanen jahar Zamfara. Shugaban Babban kwamitin rabon kayan Hon Dayyabu Adamu Rijiya ya gabatar da kayayyakin ga kananan  kwamitota na kananan hukumomi inda zasu raba su zuwa ga mutanen da zasu amfana da su. Hon Abdullahi Mohammed Dansadau tare da Hon Mansur Musa Bungudu suka rufa ma chairman na Babban kwatin baya kasancewar su Sakatare da Memba na kwamitin.

AN KASHE MUTUM 27 A ZAMFARA

Image
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Zamfara inda suka kashe mutum 27 a karamar hukumar Maradun. 'Yan bindigar sun kai harin ne a ranar juma'a cikin yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun. Tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dan malikin Gidan Goga ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar wasu matasa ne a yankin da suka dauki bindigogi suka shiga daji. "Sun iske manoma suna shuka da safe suka bude masu wuta bayan sun yi gargadin a kauracewa yin shuka a gonakin yankin," in ji shi. Ya ce lamarin ya kara muni bayan da 'yan banga suka yi kokarin kai dauki, inda 'yan bindigar suka kara kashe wasu mutane baya ga manoman da suka kashe da farko. Tsohon kwamishinan ya ce yawancin mutanen kauyukan da ke yankin, bugaje ne makiyaya da ke rikici inda suke zargin juna da sace-sacen shanu, kuma yanzu rikicin ya shafi hausawa manoma. Ya ce an tura jami'an tsaro bayan da al'amarin ya faru kuma sun janye daga yankin bayan...

REAL MADRID TA LASHE KOFIN GASAR KULOB KULOB NA KASASHEN TURAI

Image
Kulob din Real Madrid dake kasar Andulus ta lashe Kofin gasar Kulob Kulob din kasashen turai bayan da ta lallasa abokiyar hamayyata ta kasar Ingila wato Liverpool. Dan wasan kasar Faransa wato Karim Benzema ne ya fara jefa kwallo a ragar Liverpool bayan minti  56. Suma a basu bangaren, Liverpool ta farke wannan ci daga Dan wasan su dan kasar Senegal mai suna Saido Mane. Bayan wasu mintuna dan wasan Real Madrid mai suna Gareth Bale ya ci kwallo ta biyu da ta uku inda aka tashi ci Uku da Daya.

MATSALOLIN TSARO: Majalisar Dokokin Jahar Zamfara ta umurci Sakatariyar ta da ta rubuta wasika zuwa ga ministan Tsaro

Image
------------------------------------------------------------------- Majalisar dokokin Jahar Zamfara ta umurci Sakatariyar ta da ta rubuta wasika zuwa ga ofishin Ministan Tsaro domin kara sanar dashi halin  rashin tsaro da ya addabi mutanen wannan Jiha. Dan Majalisa mai wakiltar Maru ta Kudu wato Hon Abdullahi Mohammed Dansadau ne yayi wannan kira a lokacin wani zama da Majalisar tayi na gaggawa a ranarAlhamis. Hon Dansadau ya roki gwamnati tarayya da ta juyo da hankalinta a Jihar Zamfara ta hanyar turo karin Jami'an tsaro da yawa domin ganin an samu kai karshen matsalar tsaro da ta addabi jama'ar wannan jihar musamman yankin da yake wakilta. Hon Aliyu Ango Kagara shi ya goyi bayan wannan kuduri wanda daga baya Hon Malam Mani Mummuni ya kara goya  mashi baya.

SARKIN MUSULMI SA'AD ABUBAKAR YAYI TIR DA MALAMAN ADDINI DA YAN JARIDA MASU NEMAN JEFA KASAR NAN CIKIN RIKICI.

Image
------------------------------------------------------------------- Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ya yi tir da malaman addini da ‘yan jarida masu neman jefa kasar nan cikin yaki ta hanyar yada zantukan da ka iya tada zaune tsaye. Abubakar yayi wannan kakkausan gargadi ne a lokacin da ya ke jawabi da wasu al’ummar Sokoto, jami’an tsaro, malaman addini da kuma ‘yan jarida a fadar sa, a lokacin da ya gayyace su shan ruwan azumin Ramadan ranar Litinin da dare. Sarkin Musulmi ya kawo misali da wani labarin da aka buga, inda wasu Kiristoci ke cewa, “Idan Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram, to za a yi yakin addini a kasar nan.” Ya ce irin wadannan kalamai ne da ke fitowa daga bakin mutanen banza da wofi. “Ta yaya mai kiran kan sa shugaban addini zai yi wannan furuci? Ai Boko Haram ba su hada kai da musulmi suka sace yarinyar ba.” Ya tunatar da Kiristoci cewa Boko Haram sun fi kashe Musulmi sama da Kirista, nesa ba kusa ba, kuma tsohon shsugaban kasa, Goodluck Jonatha...