Posts

Showing posts from December, 2022

Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ahmad Gulak A Imo

Image
  Dubun gudajjen sojan da ke jagorantar hare-haren sari-ka-noken IPOB ya siffanta yadda ya kashe Ahmed Hula, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa. Yan sanda sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaban kasa a bangaren siyasa na zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Michael Abattam, ya ce Las Kofur Nwangwu Chiwendu, wanda dubun tasa ta cika ya gudu ne daga aikin soja ya shiga kungiyar ’yan ta’addan. A lokacin da aka yi holen sa a hedikwatar ’yan da ke Owerri a ranar Laraba, ya shaida wa ’yan jarida cewa ya shiga aikin soja a 2013, amma bayan ya samu kwarewa a fannin sarrafawa da gyaran manyan makamai, sai ya tsere a 2021 ya shiga kungiyar IPOB. “Ya zama Kwamanda a reshen soji na IPOB (ESN) inda ya horas da ’yan kungiyar sama 1,000 kan sarrafa makamai da kai hare-haren ta’addanci. “Ya amsa laifin kai hare-hare kan ofishoshin ’yan sanda da gine-ginen gwamnati a jihar nan,” in ji kakakin ’yan sa...

SOJOJIN NAJERIYA SUN FATATTAKI YAN TA'ADDA A JIHAR ZAMFARA

Image
 Dakarun sojin Najeria sun samu nasarar fatattakar "Yan ta'adda a kauyen Malele dake Masarautar Dansadau a Karamar hukumar mulkin Maru dake Jihar Zamfara. Rahotannin da muke samu daga kauyen sun nuna cewa a jiya Lahadi daruruwan maharan saman babura fiye da 400 sun dauki aniyar kai hare-hare a kauyen Malele da sauran kauyuka da ke zagaye amma hakan bai samu ba saboda dauki da Sojojin sama tare da taimakon na kasa da suka kai. Mutanen kauyukan dake kusa da wurin da abun ya faru sun tabbatar da ganin gomman gawarwakin wadannan "Yan ta'addan tare da baburan da suka hau zuwa wajen kai wannan farmakin da bai samu nasara ba, haka kuma sun shedi ganin wadanda suka ji rauni a kan babura suna gudu. Allah Ya cigaba da ba Sojojin Najeriya nasara.