Posts

Showing posts from November, 2022

Boka Ya Harbe Mai Neman Maganin Bindiga Har Lahira

Image
  ’Yan sanda a Jihar Enugu sun damke wani boka da ake zargi ya harbe wani da ya nemi maganin bindiga a wurinsa a yankin Karamar Hukumar Isi-Uzo. Aminiya  ta samu rahoton cewa, bokan ya harbe mutumin har lahira a lokacin da yake kokarin jarraba ingancin maganin bindigar da ya hada masa. Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Talata cewa, bokan ne ya kera bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe mutumin. Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna bokan ya amsa cewa lallai ya yi amfani da bindiga kirar gida wajen harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutumin a inda yake sana’arsa ta tsubbace-tsubbace. Bokan ya ce hakan ya faru ne lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada wa marigayin. Ndukwe ya ce batun na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar inda ake ci gaba da bincike.

MATSALAR TSARO A JIHAR ZAMFARA: IDAN BERA DA SATA.............

Image
Daga Sanusi Bello Dansadau Lalacewa takai matuka akama basarake wanda shine uban al'umma da hannu a cikin  lamarin kashe-kashen mutane da garkuwa dasu don kudin fansa to me ya rage Gwabnati tayi ko me mu keso ta yi?  A halin yanzu babu gari guda dake da yawan al'umma da ya kai 5000 face sai an samu masu hannu a cikin lamarin 'yan ta'addar nan wasu ma an sansu. Yakamata muyi wa kanmu fada ba Gwabnati kadai keda alhakin kawo tsaro ba muma amataki na daidaiku da al'umma munada rawar da zamu taka. Ya Allah ka tona asirin duk mai alaka da barayin nan ya Ubangiji allah ka sako mashi/su babban bala'i daga gareka Allah kayima talakka gata ka yaye muna wannan musifa amin.

Idan A Ka Cire Tallafin Man Fetur Sai Ya Koma Lita Ɗaya N410 -- NNPC

Image
  Shugaban kamfanin man fetur ta NNPC a Najeriya, Mele Kyari ya ce farashin litar mai zai kai N410 kan kowanne lita guda, maimakon N170 da ake sayarwa a yanzu, da zaran an janye tallafin mai. Kalaman Mele Kyari na zuwa ne kwana guda bayan kungiyar dillalan mai ta kasa na cewa su na son a kai farashin man naira 200 zuwa 210 domin saukaka wahalhalun mai a faɗin kasar. IPMAN ta ce janye tallafi ko karin kuɗin mai ne kawai mafita a wannan yanayi da Najeriya ke ciki. Sai dai a lokacin da ya ke jawabi a gaban 'yan majalisar wakilai, shugaban NNPC ya ce ana cikin wani yanayi saboda a halin yanzu cigaba da sayar da man kan naira 170 abu ne mai wahala, saboda farashin ya ninka haka sau uku. Don haka dole ne wani ya rinka daukan asara, kuma yanayi ne da ba zai ɗore ba. Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya. Wannan ne ya sa farashin ya sauya a cikin watanni baya, abin da ya kawo sauki a wancan l...

ZAMU KERA MAKAMIN NUCLEAR

Image
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Najariya zata yi amfani da makamin kare dangi dan samar da wutar lantarki. Ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta dukufa akan ganin wannan abu ya tabbata. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi akan makamin na Nuclear a birnin Washington DC na kasar Amurka.

YAN MATA 5 DA AKA YI GARKUWA DASU SUN SAMU "YANCI

Image
"Yan mata biyar da akayi garkuwa da su a garin Furfuri dake Karamar hukumar Bungudu dake Jihar Zamfara sun samu kubuta daga wadanda suka yi garkuwa dasu. Yaran duka diyan tsohon Akawunta Janar ne ma Jihar Zamfara. Anyi garkuwa dasu ne a watan 3 na wannan shekarar. Idan baku manta ba a watan Oktoba da ya gabata "Yanta'addar sun fitar da wani faifan bidiyon yaran tare da miyagun makamai suna barazanar jefa su cikin aikin ta'addacin idan ba'a biya kudin da suka nema a basu ba.

Ƴan Nijeriya ba su da hujjar da za su yi kukan yunwa, in ji Buhari

Image
  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ƴan Najeriya ba su da wani dalili na yin kuka a kan yunwa a lokacin da kasar ke da albarkacin katafarun filayen noma. Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin naTambari Hausa TV, wacce aka watsa a daren Laraba. A yayin da ya ke amsa tambaya kan yadda ake fama da yunwa a kasar, shugaban ya ce duk wanda da gaske yunwar ya ke ji to kuwa zai ɗauki kayan Noma ya nufi gona. A cewarsa, rufe iyakokin kasa da sauran manufofin da gwamnatinsa ta bullo da su don tabbatar da samar da abinci ya haifar da sakamako mai kyau. "Idan ku na kokarin ku kai rahoto na ga ƴan Nijeriya cewa ban cika alkawari na ba, bari in tambaye ku, lokacin da na hau mulki, ban ba da umarnin rufe iyakokin kasa ba har kusan shekaru biyu?" . “Na dauki wannan matakin ne na dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen waje, na ce mu noma abin da muke ci ko kuma mu mutu da yunwa. “Na ce tunda mu na da filin noma kuma Allah Ya albarkace mu da ruwan sama, wane ...