MAHAIFI YAYI SANADIYAR CIRE HANNUN DAN SA DAN WATA 2 SABODA YA HANA SHI BACCI A JIHAR IMO.
Wani mutumi mai suna Mr Amatobi dake jihar Imo yayi ta dukar jaririn shi mai suna Miracle saboda ya hana shi bacci wanda hakan yayi sandiyar yanke hannun jaririn sandiyar raunin da ya samu. Mahaifiyar yaron ta ce: "abun ya faru ne lokacin da na tashi domin in je in yi fitsari, ko da na dawo na same shi ya ɗaure hannun yaron bayan ya karya shi." Ta ci gaba da cewa; "da na fahimci abunda ya faru sai ya kama ni da jaririn ya rufe mu a cikin daki har tsawon kwana 2. Daga baya Allah Ya taimake ni na fita sannan na nemi mutane su taimaka mani" A lokacin da ta samu fita ta nemi taimakon mutane domin kama wannnan mutumin, inda kungiyar tsaro ta farin kaya ta kama shi amma kuma ya gudu da baya. Bayan ceton su da aka yi an kai yaron asibiti amma saboda rubuwar da hannun yayi dole aka cire shi Baki daya. Kungiyoyi da dama sun yi kira ga jami'an tsaro domin kamo wannan mutumin domin a gurfanar dashi a gaban kuliya.