Posts

Showing posts from December, 2020

SABON SHUGABAN HUKUMAR KULA DA MA'AIKATAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YA KAMA AIKI

Image
Yau Laraba 16 ga watan Disamba 2020, Sabon Shugaban Hukumar kula da Ma'aikatan Majalisar dokokin Jihar Zamfara wato Hon. Mansur A. Musa Bungudu ya kama aiki a ofishin sa dake rukununin gidajen Kwamishinoni dake hanyar bypass a garin Gusau. Shugaban hukumar Hon. Mansur Bungudu ya samu tarbo daga ilahirin Ma'aikatan hukumar wanda Sakataren hukumar Alh Chika Isiya ya jagoranta. Da yake bayani bayan gabatar da Ma'aikatan hukumar, Alhaji Chika Isiya ya bayyana halayen sabon shugaban hukumar masu kyau da nagarta kasancewar sunyi aiki tare a tsawon shekaru 8 lokacin yana Dan majalisar Jiha mai wakiltar Bungudu ta Yamma. Da yake bayani sabon shugaban hukumar, Hon. Mansur Bungudu ya yi godiya tare da neman hadin kan daukacin Ma'aikatan domin ganin Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya samu nasara a tsawon mulkin shi. Sabon shugaban ya samu rakiyar Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau, Hon. Salisu Kainuwa Tsafe, Hon. Abubakar Ajiya, Hon. Aminu Abubakar D/Jibg...

GWMANAN JIHAR ZAMFARA YA NADA SHUGABAN HUKUMAR MA'AIKATAN MAJALISAR DOKOKI TARE DA KWAMISHINAN DINDINDIN NA HUKUMAR ZABEN JIHAR.

Image
A ranar talatar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Zamfara Hon. DR. Bello Muhammad Matawalle ya mika takardar kama aiki zuwa ga Hon. Mansur Ahmad Musa tsohon Dan majalisar Jihar Zamfara mai wakiltar Bungudu ta Gabas  a matsayin shugaban Hukumar Ma'aikatan Majalisar dokoki ta Jihar Zamfara. Da yake bayani bayan karbar takardar kama aiki, Hon. Mansur Ahmad yayi godiya ga Maidaraja Gwmana tare da bashi tabbacin aiki tukuru wajen ganin an samu nasara a lokacin tsawon mulkin shi tare da bashi goyon baya ta kowa ne hauji. A dayan bangaren Hon Hashimu Shehu Gazura ne ya karbi takardar kama aiki a matsayin Kwamishinan Dindindin a Hukumar zabe ta Jihar Zamfara. Hon Gazura ya yi godiya ga Maidaraja Gwamna na damar da ya bashi domin yima jama'ar Jihar Zamfara aiki haka kuma ya nuna cikakken goyon bashi wajen ganin wannan gwamnati ta samu nasara. A cikin tawagar da suka yi wa sababbin masu mukamai sun hadu da Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau wanda shima tsohon Dan majalisar dokoki na Jihar Zamf...