Posts

Showing posts from April, 2020

DAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA MAI WAKILTAR MARU TA AREWA YA RABA KAYAN TALLAFI GA MAZABUN SA

Image
Yau Alhamis, 23 ga wayan Afirilu Dan Majalisar dokokin Jihar Zamfara mai wakiltar Maru ta Arewa wato Hon. Yusuf Alhassan Kanoma ya raba kayan tallafi ga jama'ar da yake wakilta. Tallafin da ya hada da Baburan hawa tare da injimin nika da sauran abubuwa domin rage radadin talauci ga jama'ar da yake wakilta. Da yake bayani tayin bada tallafin, Hon. Yusuf Kanoma yayi kira ga jama'ar da suka magana da suyi amfani da wadannan tallafi da suyi amfani dashi ta hanyar da ya kamata. Game da yanayi da ake ciki na annobar Coronavirus, yayi kira ga jama'a da suyi shawarwarin da likitoci suka bada akan kariya wajen kamuwa da wannan cutar. Da yake bayani, daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi ya yi godiya ga Hon. Kanoma tare da addua Allah yayi mashi jagoranci ya kuma taimake shi ya gama mulkin lafiya.

CUTAR CORONAVIRUS: INA MAFITA GA TALAKAN NAJERIYA?

Image
Daga Dr. Hakeem Baba-Ahmed     Mutane da yawa na ganin ba dole ne su bi ka’idojin da hukumomi  ke shimfidawa ba, da shawarwarin  jami’an lafiya suke bayarwa wajen kare kai daga Coronavirus, musanmam ma zama a gida, nesa da juna da wanke hannaye ba. Mafi yawan jama’a suna cewa hujjar su ita ce basu da abin da zasu biya bukatun su muhimmai idan basu fita ba, har ma da gwamutsuwar da jama’a ke yi. Wadannan hujjoji karfafa ne, kuma ya zama dole ne hukomomi   su tashi su taimaki jama’a musanman da abin da zasu ci idan sun zauna a gida har na wani tsawon lokaci kamar makonni.       Wadansu kuma gani suke ‘yancin su ne su dauki dokar da suke so, su kuma yi watsi da wadda basu so, koda kuwa suna iya bin dokokin.Wasu na kawo siyasa da hujjojin bukatar yin ibada wajen biris da dokokin tsare kai.Wasu da yawa kuma hujjar su ita ce sun gaji da zaman gida, saboda haka zasu rika fita fira ko su fita yawo inda zasu hadu da sauran mutane.   ...