YADDA ZA'A SHIRYAR DA YARA DABI'U MASU KYAU
1. Ku dinga shiga gida da sallama, inda hali ku sumbanci yaran ku, wannan zai sa musu kauna da sanin kiman kan su. 2. Ku zama masu kyakkyawar mu'amala ga makwabtanku, kada ku zama masu gulma da rada, kar ku fadi munanan magana ga masu abin hawa a kan hanya. Yaran ku suna ji, za su koya kuma zasu dauka su dinga yi. 3. Duk lokacin da za kuyi magana da iyayen ku a waya ko za ku ziyarce su ku tabbatar kun yi tare da yaran ku, domin hakan zai sa yara su koyi jin ƙai da kuma tausaya muku don sun ga yadda kuke yi wa naku iyayen. 4. Lokacin kai su makaranta kar ku yawaita sa musu kide kide da waƙoƙin sharholiya, ku yawaita basu labarai da kissoshi da zai ankarar da su Al'amurra na gari, Ina tabbatar muku zai taimaka sosai! 5. Karanta musu guntayen labarai ko wani guntun tarihi a ko wane rana, ba zai ci lokaci ba amma yana taimaka musu wajen nitsuwa kuma yana kama zuciyar su. 6. Ku tsaftace kan ku da Wanka da wanke baki da taje kai da sa kyawawan tufafi (Kaya) ko da kuwa ...