AJANDAR ABDUL'AZIZ YARI TA NEMAN ACE YAFI KOWA KUDI A JIHOHIN SOKOTO, KEBBI DA ZAMFARA TA BAYYANA A FILI.
Daga Ibrahim Bello Gusau . Jihar Zamfara tana Daya daga Cikin Jihohin tarayyar Najeriya a Yankin arewa maso yamma Mai jihohi Bakwai, Jihar Zamfara tana Daya daga Cikin Jihohin da aka kirkiro a Shekarar 1996 a lokacin Mulkin Soja na Janaral Sani Abacha. Daga Shekarar da aka kirkiro Jihar Zamfara Zuwa yau tayi Gwamnoni na farar Hula Guda hudu, wato: Alh Ahmad Sani Yariman Bakura daga 1999-2007. Alh Mahmoud Aliyu Shinkafi daga 2007-2011 Alh Abdul'aziz Yari daga 2011-2019 Alh Hon Dr Bello Matawallen Maradun Watan mayu 2019 Zuwa Yau. Al'ummar Jihar Zamfara Sun Shedi Salon Mulkin Duk Wadannan Shugabannin Kuma zasu iya tarfa albarkacin bakinsu akan haka. Salon Mulkin Yariman Bakura na tallafama Jama'a ne da neman suna a idon duniya. Salon Mulkin MAS Kuma na Kokarin Gina Jihar Zamfara ne sai dai akwai Sakaci da ko inkula. Salon Mulkin Abdul'aziz Yari na atara Kudi ne a hana al'umma Walwala tareda tauye su, Wannan shine ya kawo Girman Kai, Wulakanta M...