Posts

Showing posts from February, 2019

KA TSAYAR DA YAN TAKARAR MU KO MUKI BAKA ƘURI'UN MU: GARGADIN GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA ZUWA GA BUHARI

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Sakamakon rikita-rikitar da ake ciki na rashin samun Yan takarar jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta dauki sabon salo inda jami'an gwamnatin suka yanke hukuncin ba zasu zabi shugaba mai ci yanzu ba wato Buhari in har bai tsayar masu da Yan takarar su ba. Alamu sun nuna haka ne a lokacin da aka shirya zaben Shugaban Kasa yare da na Yan Majalisun tarayya inda bayanai sirri suka nuna an turo da kudin da ya kamata a ba wadanda zasu wakilci Jam'iyyar a runfunan jefa kuri'a amma gwamnan ya hana a baryar da kudin. Bayanan da muka samu game da kudin shine gwamnan ya bukaci da a bashi kudin a hannu ba tare da an tura su ga asusun ajiya na Jam'iyyar APC ba Amma hakan bai samu ba sai dai aka tura a asusun ajiya na Jam'iyyar APC. Yanzu haka dai shugabannin Jam'iyyar APC a bangaren gwamnati suna nan suna ganawar sirri tun daga matakin mazabu har zuwa na jiha domin ganin yadda zasu bullo ma zaben da za'a yi ranar Asabar 23/2/2019 ka...

DUK DA ODAR DA BABBAN KOTUN JIHAR ZAMFARA TA BADA: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA RIKE MA WASU YAN MAJALISA ALAWUS

Image
. Daga S. Sadiq, Gusau. Alamu ya nuna cewa Majalisar dokokin Jihar Zamfara bata yi amfani da odar da Babban Kotun Jihar Zamfara ta bayar ba karkashin jagorancin Alkali Bello Aliyu Gusau. Rahotannin da muke samu sun nuna cewa akwai wasu hakkokan su da aka rike masu wadanda suka kun shi alawus nasu da suke karba daga Ma'aikatar kananan hukumomi. A wani rahoton kuma ya nuna cewa Majalisar dokokin ta kuduri rike masu  alawus wanda ake kira da suna C.A wato Cash Allocation kenan a turance. Da ya ke hira da wani lauya mai zaman kan shi a Gusau Babban Brinin Jihar, Barrister Rabiu Magaji ya ce Babbar Kotun na da hurumin da zata dauki kwakkwaran mataki na hukunta duk wani mai sa hannu wajen rike masu hakkokin. Lauyan ya kara da cewa bijirewa odar babban laifi ne wanda yana iya jawo hukunci mai tsanani.