Posts

Showing posts from September, 2018

GASKIYAR ABINDA KE FARUWA A DAJIN ZAMFARA.

Image
Daga Mustapha Sarkin Kaya A safiyar Assabar Hadakar Kungiyoyin Sakai da suka hada da Yan Farauta da Maharba, Daga Arewacin Zamfara da gabashin Sakkwato Suka Shiga Dajin da ya hada Zamfara da Sakkwato wato Dajin Gundumi Inda aka kwashe yinin Jiya Assabar Ana fafatawa. Duk dayake Wannan Aiki yasamu matsala ta hanyar Rashin Shigar Sirri, domin Mahara Sun samu labarin zuwan Yan sakai tun a lokacin da suke kan hanyar Shiga Dajin, wannan lallai ya sababba kwantan 6auna da 6arayin sukayi, a karon farko lallai sunyi barna ga Gungun yan sakai Musamman ga Wadanda sukayi kokarin Dawowa baya. Amma yazuwa Yau lahadi Akwai labari Mai kyau akan wannan fafatawa Ansamu galaba sosae, yazuwa Yanzu Mun samu labarin Mashuna fiye da Dari biyu da aka kona tare da kashe 6arayi da ba'asan adadi ba. An karbo bindigogi Ak47, fiye da Saba'in, an karbo Manyan bindigogi Masu Jigida, kuma har Yanzu Suna bakin fama. Ansamu Gungun wasu Yan sakai da suka Hadu da Safiyar Yau Lahadi a Garin Teke ...

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA SHA RUWAN DUWATSU

Image
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya sha ruwan duwatsu  ga wasu gungun matasa masu goyon bayan Jam'iyyar APC a garin Gusau hedikwatar Jihar. Wannan ya biyo bayan shigowa  da yayi da tawagar sa a lokacin da Magoya bayan "yan takarar gwamna a karkashin Jam'iyyar APC a jihar har su bakwai suka tarbo su daga garin 'Yankara dake iyaka tsakanin Jihar Katsina da ta Zamfara. Da muke zantawa da wani da abun ya faru a gaban sa yace gwamnan yana zuwa sai matasan suka fara ihu suna kiran shi da 'barawo....barawo bamuso ....bamu so! Abun yayi kamari har sai da jami'an tsaron sa suka yi ta harba bindiga a sama domin korar wadannan matasa. Idan baku manta ba, siyasa a jihar Zamfara tayi zafi inda shi gwamnan ya ayyana cewa kwamishinan kudin Jihar zai gaje shi wanda wannan hukuncin bai yi wa sauran yan takarar dadi ba wanda shine dalilin da ya sa suka hadu wuri daya domin tunkarar wanda gwamnati ta tsayar.