LARURAR DANNAU WATO SLEEP PARALYSIS
Daga Ibrahim Y. Yusuf Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu ahalin bacci, yakan iya faruwa sau daya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan rika fuskantar yanayin akai-akai. Yanayi ne me kama.da mutuwa duk da yakan kasance mutum na acikin hayyacinsa farke saide sam yakan rasa ikon motsawa ko magana. Wani lokacin ma yakan zamo idon mutum abude zahiri duk da cikin bacci yake; abunda wasu kan kira da bacin zomo... toh saide hakan duk baisa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa yana cikin mawuyacin hali ko yana bukatar dauki an maquresa. Shiyasa ga duk meson fahimtar me ake nufi da FIRGICI toh dannau shine cikakken misalin firgici ko ince ihunka banza domin ko ihun kayi ba'a ji, ba'a san ma kanayi ba ALAMOMIN DANNAU Mutane kan fuskanci ma bambantan alamu; Saide duk yana daga alamun dannau ya zamto: ■- Mutum yaji kamar annan-naɗesa cikin wani bargo me nauyi, ko kamar anɗaure hannuwa da kafafunsa a mike kamar gawa, wasu kuma suji kamar anshakesu sun...