Posts

Showing posts from August, 2021

HARIN MAKARANTAR KOYON AIKIN SOJA: Hakika Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami'an tsaron mu sun tafka abin kunya!!

Image
Daga Comrd S-bin Abdallah Sokoto. Idan har 'yan bindiga zasu iya kai farmaki a wannan makaranta ta NDA dake Kaduna to tabbas lamarin tsaro a kasar nan ya yi mummunar lalacewa. Na rantse da idan har Gwamnatin Najeriya bata tashi tsaye ta hallaka wadannan 'yan bindiga ba watatana sai ka ji sun yi garkuwa da Gwamna ko shi kan shi shugaban kasa Muhammadu Buhari din. Hakika wannan hari zai yi matukar cirewa al'ummar karkara tsammanin samun tsaro  da suke fatan ganin sun samu a kowace rana ta Allah. Buhari ka ji kunya! Gwamnonin Arewa kun ji kunya! Sanatocin Arewa kun ji kunya!. Maciya amanar Arewa kun ji kunya!. Allah ya isarma talakkan Najeriya da ya sha rana ya zabe ku.

RUNDUNAR SOJIN SAMA TA HALLAKA BARAYIN DAJI A DAJIN KUYAMBANA

Image
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun yi luguden bama-bamai a kan sansanonin 'yan fashin daji cikin jihar Zamfara - har ma sun kashe aƙalla saba'in da takwas. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, sojojin saman na Najeriya sun ce wasu daga cikin 'yan fashin dajin kuma sun tsere yayin samamen. Ta ce hadin gwiwar dakarun tsaron sun kwashe tsawon kwana uku tun daga ranar Litinin har zuwa Laraba suna lugude a kan 'yan fashin dajin - waɗanda suka addabi yankin. A cewar rundunar luguden bama-baman ya shafi sansanonin 'yan fashin dajin da ke cikin dajin Kuyanbana, kudu da garin Ɗansadau cikin ƙaramar hukumar Maru. Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan fashin daji a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a sassa da dama na jihohin Neja da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Katsina da kuma Kebbi. Rundunar sojin saman Najeriya dai ta ce yayin wanna...

DANSADAU: Jiya da Yau.

Image
Daga Mohammed Kabir  Dansadau gari ne da Allah Ya albarkata da abubuwa kala-kala. Daga girman kasa zuwa yawan jama'a, albarkatun kasa, filin noma da kiyo da sauran abubuwan habaka tattalin arziki. A kimanin shekaru 15 zuwa 20 da suka gabata a duk fadin jihar Zamfara babu yankin da aka yi itifakin ya ke samun cigaba kamar wannan yanki, sai dai kash! yanzu labari ya canza kasancewar halin da kasar ta samu kanta na mummunar matsalar tsaro a cikin kusan shekaru goma da suka wuce. A halin da ake yanzu yawan hare- haren da ake kawo ma wannan garin yayi sanadin mutane da yawa suna gudun hijira daga garin zuwa wasu garuruwan domin tsira da rayukan su. Daga watan Janairu na wannan shekarar zuwa watan 7 anyi garkuwa da mutane fiye da 500 a wannan yanki, wasu matafiya wasu kuma mazauna garin inda aka kashe mutane da yawan su. A cikin watan da ya gabata, a kauyen Kabaro da yake cikin gundumar Dansadau 'Yan ta'adda suka harbo jirgin saman yaki na sojojin Najeriya wanda wannan ba karamin...