KIWON LAFIYA: CUTAR SANKARA KO DAJI
Daga Aliyu Samba. Cutar sankara ko cancer da turanci na daya daga cikin cututtukan da ke adabar al’umma a wannan zamani, kuma cuta ce da take da matukar wuyar sha’ani. Cutar Sankara Babbar matsala ce a cikin al’umma saboda yawan kawo jinya da rashe-rashen rayuka da take yi. Wasu ana iya kare kai daga kamuwa da su, wasu kuma sam haka nan kawai suke kama mutum, musamman idan yana dauke da nakasa a cikin kwayoyin halittunsa na gado. Cutar ta sankara tana da nau’o’i daban-daban saboda tana kama sassa daban-daban na jikin mutum. Ga manya daga cikin sassan jiki da cutar ta fi kamawa a wannan kasa tamu. A) MAZA: 1- Sankarar halittar Prostate Gland. 2- Sankarar Hanta. 3- Sankarar kwayoyin Jini. 4- Sankarar Hanji B) MATA: 1- Sankarar Nono 2- Sankarar Bakin Mahaifa. 3- Sankarar kwayoyin halittu na obary (kwan mace). 4- Sankarar Hanji. C) YARA: 1- Sankarar Kumatu. 2- Sankarar kwayoyin Jini. 3- Sankarar Ido. 4- Sankarar kashi A Najeriya dai an fi samun cancer ta mahai...