HON. ABDULLAHI MUHAMMAD DANSADAU NE SHUGABAN NASIRIYYA NA JIHAR ZAMFARA
Daga Abubakar A. Zaria, Kaduna. Wata kungiya mai fafatukar ganin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya zama shugaban wannan Kasar a shekara ta 2023 ta zabi Hon Abdullahi Muhammad Dansadau a matsayin wanda zai jagoran ci wannan tafiyar a jihar Zamfara. Bayan Mika mashi takardar nadin na shi, Hon. Dansadau ya bada tabbacin bada gudumuwar sa ganin an samu nasara ga wannan tafiya ta hanyar tabbatar da Malam Nasir El-Rufai ya samu damar hawa kujerar shugabncin Najeriya a zabe mai zuwa. An haifi Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau a shekara ta 1977 a garin Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Yayi karatun sa na Firamare a da Sakandire a garin Dansadau daganan ya cigaba zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha dake Talatar Mafara inda ya karancin fasahar Kididdiga wato Accounting. Ya cigaba zuwa Jami'ar Bayero dake Kano inda ya karancin babbar Diploma wato PGD duka a fannin Kididdiga. Daganan ya wuce zuwa Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria inda yayi Digirin d...