KIRA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA ABDULAZIZ ABUBAKAR YARI
Daga Ibrahim Bello Gusau IBG. A cikin mutun ta wa da girma ma wa na ke mika sakon tunatar wa zuwa ga mai girma gwamnan jahar zamfara, Hon. Abdul'aziz Yari Abubakar, akan cewa zamfara jaha ce ta shari'a kuma kaso mafi tsoka na al'ummar ta musilmai ne da ba su chanchanci a raba su da karantarwar shari'ar da Allah ya saukar zuwa gare su ba. A kwanakkin nan ne mu ka ji kwamishinan lamurran masarautu da kananan hukumomi na jahar zamfara , Alhaji Dankande Gamji, ya ba da sanarwar wani aikin hadin guiwa inda za a gayyato malamman tsibbo da bokaye domin daure daji, da kuma baiwa yan sa-kai maganin bindiga da kuma layar zana a wani mataki na raba jahar zamfara da yan ta'adda ma su kisan gilla ga al'umma tare da garkuwa da su wanda wannan ya ci karo da akidar musulunci sannan kuma hakan yana iya raba al'ummar musulmi da addinin su na musulunci da sunan kare rayukka da dukiyoyin al'umma. A sani ba wata rayuwa ko dukiya da musulmi zai yi hasara kuma ...