NAIRA DUBU BIYAR (N5,000) AKE BIYANA A DUK LOKACIN DA NA SHIRYA AKA KAI ƘUNAR BAKIN WAKE, INJI WANI WADA...
Daga Shafin Datti Assalafiy Wani wada ɗan kungiyar boko-haram da aka kama mai suna Abubakar Kori, wanda yake shirya yadda ake kai harin ƙunar bakin wake yace Bai taɓa karɓan kasa da naira dubu biyar ba akan kowace harin ƙunar bakin wake da yake shiryawa yan ta'addan kungiyar boko-haram a birnin Maiduguri. Abubakar Kori, ɗan shekara 25 yana ɗaya daga cikin mutane 22 da jami'an ƴan sanda suka kama a jihohin Borno da Yobe, sakamakon samun su da hannu da akayi wurin kai hare-haren ƙunar bakin wake da ƴan ta'addan boko-haram keyi. Ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa naira 5000 ake biyan shi a duk lokacin da ya shiryawa ƴan ta'addan yadda zasu kai hari tare da samun nasara, a birnin Maiduguri da kewaye. Abubakar Kori, Wanda shi mai gadi ne a wani gidan mai a yankin unguwar Dalori dake birnin Maiduguri, Yace yana da hannu a wasu hare-haren ƙunar bakin wake da aka gudanar a ƴan kwanakin nan a birnin na Maiduguri. ~Isa Ade Allah Sarki, wat...