AN KARRAMA SHUGABAN JAMIYYAR AFRICAN DEMOCRATIC CONGRESS NA JIHAR ZAMFARA.
Sananniyar kungiyar cigaban matasa dake shiyar Mayana a cikin garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara wato Mayana youth development association ta karrama shugaban Jam'iyar ADC na Jihar Zamfara Hon Kabiru Garba a babban ofishinta dake garin Gusau. Da yake gabatar da takardar shedar karramawa, shugaban kungiyar yace: "mun karramaka ne a saboda gagarumin taimakon da kake bayar wa wajen cigaban matasa a wannan jihar". Haka kuma ya kara da cewa "tabbas mutane da dama sun amfana da ayukkan alkhairan da ka keyi a cikin Jihar Zamfara". Da yake karbar kyautar, Hon. Kabiru yayi godiya ga shugabanni tare da sauran "Yan kungiya na wannan karamci da suka mashi ya kuma bayyana cewa zai kara kokari da himma wajen ganin ya kawo cigaba ga matasan Jihar Zamfara da Najeriya baki daya. Dantakar Gwama a karkashin Jamiyyar ADC Dr. Ahmad Hashim Tsanu tare da sauran Yan takarkari da daruruwan magoya bayan Jam'iyyar sun samu halartar taron.