DR AHMAD GUMI A DAJIN TAGINA DA YA HADA NIGER DA KADUNA TA BIRNIN GWARI.
........ NA YARDA DA MAGANAR SULHUNKA KUMA ZAN FARA AIWATARWA - DOGO GIDE. Daga Salisu Hassan Webmaster. Alhamdullah! Yau Allah ya taimaki Dr. Ahmad Gumi da tawagarshi samun damar ziyartar garin Mina inda ya isa Kontagora daga nan ya karasa dajin Tagina inda suka yi mahada da Shugaban Daji (Dogo Gide). Wannan daji ne da ya hada garin Niger da Kaduna ta wurin Birnin Gwari. Nasihohi daga bakin Sheikh Dr. Ahmad Gumi game da muhimmancin yin Sulhu da kuma haramcin yaki a wannan wata da kuma rokonsu game da ajiye makamai da haramcin yin fasadi a bayan kasa. A nashi jawagin Dogo yace wannan shine zama na farko da aka yi da shi game da irin wannan sulhun kuma ya yarda ya dauka, kuma yana shaidawa malam zai fara aiwatar da wadansu. Dogo Gide ya shaidawa malam irin abubuwan da suke nema wanda idan aka yi musu shi zasu saki mutanen da suke hannunsu. Duk da ba su bari an dauki video na wannan tattaunawa ba, amma sun bayar da damar daukar sauti na wannan tafi, kuma da zarar mun kammala g...