Posts

Showing posts from July, 2019

Zamfara: Mun Yi Allah Wadai Da Kalaman Yari

Image
In ji Dr. Aslam Aliyu Daga Jaridar 'Yanci Babu shakka mu al’ummar jihar Zamfara, muna cike da farin ciki, tun bayan darewar Gwamna Dr. Matawalle, musamman ganin yadda kullum ake samun nasara dangane da abubuwan da suke damun mu a wannan jiha. Tabbas addu’ar da muka dukufa muna yi ce tasa Allah ya dubi halin da muke ciki ya kawo mana wannan bawan Allah Gwamna Matawalle. Hakika irin kalaman tsohon Gwamna Abdulaziz Yari abin takaici ne ga al’ummar arewa ma a iya jihar Zamfara ba. Domin ya kamata Gwamna Yari ya san cewa, Gwamnati fa gaskiya ce, kuma sulhu alkairi ne. Mun yi asarar rayuka, dukiyoyi da sauran abubuwa da dama a jihar Zamfara, duk ta sanadiyar wadancan rikice-rikece, amma cikin ikon Allah Yanzu komai yana sauka kasa, suna ci gaba da ajiye mukaman su. Ba za mu so a ci gaba da jib da jini a jihar Zamfara ba, domin wannan jinin Iyayen mu ne da ‘yan uwan mu Musulmi. Abin takaici ne matuka, yadda Tsohon Gwamna Yari yake fito da hanyoyin bata Gwamnatin Dr. Bel...